Gwamnati ta kwace iko da filin jirgin Donestk

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Filin saukar jiragen sama na Donetsk

Gwamnatin Ukraine ta ce dakarunta sun sake kwace iko da filin jirgin saman dake garin Donestk na gabashin kasar.

A cewarta dukka wadanda aka kashe a gumurzun, 'yan aware ne magoya bayan Rasha.

Oleksandr Scherba jakada ne na kasar ta Ukraine, ya na cewa ne "Abin da ke gabanmu shi ne tattaunawa da Rasha, da zarar muka fatattaki sojojin haya na kasar Rashan daga yankin kasarmu, inda suke jagorantar kai hare hare."

'Yan bindigar da suka kwace iko da filin jirgin saman, a ranar Litinin, sun ce an kashe sama da mayakansu 30, a lokacin da dakarun gwamnati wadanda jiragen saman yaki ke rufa ma baya suka kaddamar da hare hare a kan su.

Shugaba Putin ya yi kiran da a dakatar da farmakin sojin da dakarun Ukraine ke kaiwa a gabashin kasar, a kuma tattauna tsakanin sabbin shugabannin da kuma 'yan aware masu goyon bayan Rasha.

Karin bayani