'Mun san inda aka boye 'yan matan Chibok'

Babban Hafsan Hafsoshin Tsaron Najeriya Air Marshal Alex Badeh Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Sojojin sun ce ba za su bayyana inda 'yan matan Chibok din suke ba saboda gudun kada a jefa rayuwarsu cikin hadari

Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta san inda ake tsare da 'yan matan nan fiye da 200 da kungiyar Boko Haram ta sace a jihar Borno.

Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriyar, Air Marshal Alex Badeh ya ce ba za su yi amfani da karfin ba wajen kubutar da su.

Badeh ya shaida wa masu zanga-zangar neman a dawo da 'yan matan a Abuja cewa, ba zai bayyana inda ake tsare da su ba, amma ya yi alkawarin cewa sojoji za su kubutar da su.

Sace 'yan matan dai ya haifar kakkausar suka daga kasashen duniya, da zanga-zanga daga kungiyoyi daban-daban a ciki da wajen kasar, don zaburar da mahukuntan Najeriyar su kara hobbasa wajen ceton 'yan matan.