Al-sisi ya lashe Zabe a Masar

Abdul Fatta al-Sisi
Image caption Al-sisi dai shi ne ya jagoranci hambarar da gwamnatin shugaba Muhammad morsi.

Kafar yada labaran kasar Masar ta rawaito cewa tsohon shugaban hafsan sojin kasar Abdel Fatta al-Sisi ya yi nasarar lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a makon nan.

Kafar yada labaran sakamakon zaben ya nuna cewa Al-sisi ya samu sama da kashi casa'in na kuri'un da aka kada a kasar.

Haka kuma kuma an bayyana cewa daman ba a taba shakkun cewar Al-sisi ne zai yi nasara a zaben ba, ya samu gagarumin goyon baya daga wadanda suka jefa kuri'a.

Sai dai a bangare guda kungiyar 'yan uwa Musulmi da wasu kungiyoyin sun kauracewa zaben.

Duk da haka an bayyana cewa kasa da kashi arba'in da biyar cikin dari na al'umar kasar ne suka fito zaben duk da cewa an kara kwanakin zaben da kuma bawa mutane tikitin jirgin kasa kyauta dan fita kada kuri'ar.

Wakilin BBC a birnin Alkhahira yace kokarin da gwamnati ta yi na ganin an fito zaben ya sanya ayar tambaya a zukatan mutane kan sahihancin daukar matakin.