Chibok: An kai wa masu zanga-zanga hari

Image caption Ga alamu dai babu wanda ya jikkata sakamakon harin.

Wani gungun mutane da ake zargin magoya bayan gwamnati ne ya kai wa taron masu zanga-zangar neman a kubutar da 'yan matan Chibok a Abuja hari.

Wani wakilin BBC da ke wurin ya ce maharan sun yi wa masu zanga-zangar duka tare da kakkarya kujerun da suke zama da su a dandalin Unity Fountain da ke tsakiyar babban birnin na Najeriya ranar Laraba.

kungiyar masu zanga-zangar ta Bring-back-our-girls karkashin jagorancin tsohuwar ministar ilmin kasar Oby Ezekweseli, na zargin cewa 'yan koren gwamnati ne suka kai musu hari da nufin wargaza musu tafiya; amma ta ce hakan ba zai sa su fasa ba.

Kafin wannan harin dai ministan yada labaran Kasar Mr. Labaran Maku ya soki lamirin Kungiyar Bring Back Our Girls da cewar kashi 90% nasu 'yan wata jam'iyyar siyasa ne.

Karin bayani