Al Shabab ta dauki alhakin harin Djibouti

Mayakan Kungiyar Al Shabab Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mayakan Kungiyar Al Shabab

Kungiyar Al Shabaab ta kasar Somalia ta ce ita ce ta kai harin Djibouti, a wurin cin abinci inda baki suka fi yawa.

Harin na a ranar Asabar da daddare da ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutum uku, ana kyautata zaton biyu daga cikinsu ne suka kai harin na kunar bakin wake.

Baki 'yan kasashen waje da dama ne suka samu raunuka a harin.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Al Shabab ta ce ta kai harin ne a wannan wurin da ke zaune a Djibouti.

Kungiyar na zargin kasar Faransa da ta kasance mai mafi yawan sojoji a Djibouti, da zargin gallazawa Musulmi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.