Ebola: Likitoci sun isa Saliyo

Hakkin mallakar hoto AFP

Likitocin dake kan hanyarsu ta zuwa gabashin Saliyo sun fito ne daga hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya wato WHO da kuma kungiyar agajin likitoci ta Medicin San Frontiers.

Cutar Ebola dai tana wuyar sha'ani saboda saurin yaduwarta. Koda taba jikin wanda yake dauke da cutar, zai haddasa kamuwa da cutar cikin gaggawa.

Dan haka jami'an kiwon lafiya da zasu yi aikin shawo kan cutar sai sun lullube jikinsu daga sama har kasa, wanda lamari ne mai wuyar gaske saboda tsakanin zafi a irin wadannan kasashe.

Sai dai kuma jami'an kiwon lafiyar suna fuskantar wani babban kalubalen tun ma kafin su soma yin aikin.

Bayan cutar ta Ebola ta barke a Saliyo a farkon wannan makon dangin wasu mutane shida da suka kamu da suka kamu da cutar sun dauke 'yan uwan nasu daga asibiti.