Boko Haram: Ghana na shirin ko-ta-kwana

Shugaban Ghana, John Mahama Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana zargin Boko Haram da kai hari a Kamaru, kasar da ke makwabtaka da Najeriya

Kasar Ghana ta fara saka sojojinta cikin shirin ko-ta-kwana domin tunkarar matsalar Boko Haram ko da za ta bulla a can.

A wata ganawa da ya yi da manyan hafsoshin sojan kasar a birnin Accra a ranar Talata, Shugaba John Mahama ya ce gwamnati na kokarin sama musu kayan aiki na tunkarar kalubalen.

Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da fuskantar barazanar 'yan kungiyar Boko Haram a kasashe da ke makwabtaka da Najeriya, inda ta fi karfi.

Sannan ana ganin akwai yiwuwar fadadar kungiyar zuwa wasu kasashen, musamman wadanda suka hada iyaka da Najeriya.

Karin bayani