Ana ci gaba da binciken Jirgin Malaysia

Dandazon masu yin addu'a akan batan jirgin Malaysia Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jirgin Malaysian ya bata ne fiye da watanni uku kuma har yanzu ba a ji duriyarsa ba.

Rundunar sojan ruwan Amurka ta yi fatali da wasu kalamai da wani babban kwamanda ya yi game da binciken jirgin saman malaysian nan da ya yi batan dabo a matsayin shaci-fadi da kuma kalaman da bai dace a yi ba.

Mataimakin Daractan da ke kula da Sojin ruwa Mike Dean yace sautukan da aka ji wadanda aka ce ana kyautata zaton a nan wurin jirgin ya ke ta yiwu na jirgin ne ko kuma tarkacen jirgin kansa.

Ya yi wannan jawabi ne bayan da masu aikin binciken jirgin a kudancin tekun India suka isa wuri na karshe da suke gudanar da aikinsu na baya-bayannan.

Kakakin rundunar Sojin Ruwan Amurka yace za su ci gaba da aiki kafada-da-kafada da sauran tawagar da ke binciken,kuma ya rage ga kasar Austarlia da ke jagorantar binciken da ta fitar da wani sabon bayani.