Jonathan na jimamin rasuwar Sarkin Gombe

Hakkin mallakar hoto Facebook
Image caption Margayi Sarkin Gombe, Alhaji Usman Shehu Abubakar

Shugaban Nigeria, Dr Goodluck Ebele Jonathan ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan marigayi mai martaba Sarkin Gombe, Alhaji Shehu Abubakar.

Shugaban ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da fadar gwamnatinsa ta fitar a Abuja.

Mr Jonathan ya ce ya tuna da irin karramawar da marigayin ya yi masa a lokacin da yaje taron tattalin arzikin yankin arewa-maso-gabashin kasar a Gombe a bara.

Mai martaba Sarkin Gombe, Alhaji Shehu Usman Abubakar, ya rasu ne da safiyar ranar Talata a birnin London.

Kafin rasuwarsa shi ne kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Gombe.