Daliban kwalejojin Nigeria sun yi bore a Lagos

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Wasu daliban makarantun Kimiyya da fasaha da Kwalejojin ilimi, sun gudanar da wata zanga-zanga a birnin Lagos.

Daliban na neman a kawo karshen yajin aikin da malamansu ke yi tun kusan watanni 10 da suka wuce.

Malaman masu yajin aiki na neman a inganta yanayin aiki da kuma albashinsu.

A nasa bangaren ministan kwadago Emeka Nwogu ya bayar da tabbacin cewa, gwamnatin kasar na daukar duk matakan da suka dace domin cimma yarjejeniya da kungiyoyin.