Marubiciya Maya Angelou ta rasu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Margayiya Maya Angelou

Marubuciyar nan ba Amurkiya, kuma malamar Jami'a, Maya Angelou ta rasu tana da shekaru tamanin da shidda.

Kashin farko na littafin da ta rubuta kan rayuwarta,'I Know Why the Caged Bird Sings', na bayyana irin matsalolin da ta ci karo da su ne a wani zamani da aka yi fama da matsalar wariyar launin fata.

Littafin ya kasance sahun gaba wajen samun kasuwa watau 'Best seller'.

Iyalanta sun ce "Ta yi rayuwa a matsayin malamar makaranta kuma mai fafutukar kwatar 'yanci".

Sanarwar da suka fitar a shafin Facebook, ta ce Angelou ta rasu a gidanta da ke Winston-Salem a jihar North Carolina.