Bauta: Dan Nijar zai yi shekaru 4 a kurkuku

Image caption A mafi yawan lokuta ana sa bayin ayyukan kiwon dabbobi na iyayen gidansu makiyaya

A karon farko an yankewa wani dan Nijar mai shekaru 63 hukuncin shekaru hudu, a kurkuku bayan samunsa da laifin bautar da wata mata.

A al'adar Azbinawa masu kudin cikinsu na iya sayen yarinya baiwa a matsayin mace ta biyar, amma babu aure a tsakaninsu kuma za a tilasta mata yin ayyukan karfi.

Sai dai wanda aka samu da laifin an yi masa sassauci saboda ya nuna nadama, kuma daga bisani ya auri yarinyar.

Wata kungiya da ke yaki da bauta ta yi kiyasin cewa akwai bayi dubu 40 a Nijar, kuma da dama daga cikinsu an haife su ne cikin bautar.

Kungiyar ta ce wannan ne karon farko da aka taba samun wani da laifi, tun bayan haramta bautar a shekarar 2003.