Yarinya ta gudu daga hannun Boko Haram

Wasu iyayen 'yanmatan da Boko Haram suka sace Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu iyayen 'yanmatan da Boko Haram suka sace

Rahotanni daga jihar Borno arewacin Nigeria Nigeria sun ce a yammacin ranar Talata wata yarinya ta kubuta daga hannun 'yan kungiyar Boko Haram.

Koda yake daya daga cikin shugabannin al'ummar Chibok -- Dr Pogu Bitrus wanda ya ba da rahoton kubutar yarinyar -- ya ce ba daya daga cikin 'yan matan makarantar Chibok da ake ta cece-kuce a kansu ba ne.

Mr Bitrus ya bayyana cewar kubutar da yanzu 'yan matan biyar suka yi tun daga makon jiya abu ne mai karfafa gwiwa.

Kafin sace 'yan matan makarantar ta Chibok dai 'yan kungiyar Boko Haram sun sace mata da 'yan mata da yawa a sassan jihar daban-daban.