Ana zaman dar-dar a Bangui

Hakkin mallakar hoto
Image caption Musulmi da Kiristoci na kashe juna a Bangui

Zaman dar dar na karuwa a Bangui babban birnin Jamhuriyar Afirka ta tsakiyar sakamakon wani mummunan hari da aka kai kan wani Coci a ranar laraba.

Mazauna birnin sun ce, babu cinkoson ababen hawa, kuma jirage masu saukar Angulu na sojin Faransa na ta shawagi kasa-kasa a saman birnin.

Mutane da yawa dai na tsoron barkewar wani sabon tashin hankali duk da kasancewar dakarun kiyaye zaman lafiya na Afrika da Faransa.

Kungiyar 'yan tawayen Seleka ta galibi Musulmi na sake haduwa a arewa maso gabashin kasar domin abinda ta ce, sa ido sosai a kan mayakanta.

Karin bayani