'Yan ci-rani na karuwa a Tarayyar Turai

'Yan cirani daga Africa da suka isa tsuburin Lampedusa na Italia Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan cirani da dama dai na gamuwa da ajalinsu tun kafin su isa tarayyar turai.

Kididdigar da hukumar kula da iyakokin Tarayyar Turai da gwamnatin Italiya suka fitar ta nuna cewa fiye da mutane 60,000 ne suka tsallaka iyakokin nahiyar a watannin farko na wannan shekarar ba bisa ka'ida ba.

Hukumar Frontex ta bayyana cewa akalla 'yan ci-rani 42000 ne suka shiga Turai ba bisa ka'ida ba a rubu'in farko na wannan shekarar,wanda ya hada da 'yan ci-rani da ke yin kasadar shiga kassahen turai ta tekun arewacin Afrika da Italiya.

Hukumar Frontex ta kara da cewa akwai yiwuwar adadin 'yan ci-ranin ya karu a cikin lokacin bazara.

Rahotanni na nuna cewa za a iya samun fiye da mutane 300,000 a kasar Libya da suke sa ran tsallakawa kasashen turai.

Karin bayani