'Dimokaradiyya na fuskantar barazana'

Image caption Jonathan ya ce kungiyoyin ta'addanci na barazana ga mulkin dimokaradiyya

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan, ya ce dimokaradiyyar kasar da aka kwashe shekaru 15 ana cin moriyarta tana fuskanta barazana daga hare-haren 'yan ta'adda.

Mista Jonathan ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi wa 'yan kasar ranar Alhamis.

A cewarsa, abin takaici ne ganin cewa kwanaki 45 kenan da sace 'yan matan makarantar Chibok da ke jihar Borno amma har yanzu babu duriyarsu.

Shugaba Jonathan ya sha alwashin ceto 'yan matan, yana mai taya iyayen 'yan matan nuna bakin ciki game da sace su.

'Nigeria na yaki da 'yan Al-Qaeda'

Shugaba Jonathan ya yi kira ga kungiyoyin da ke kai hare-hare da su daina, yana mai shan alwashin yin sulhu da su idan suka yi hakan.

Ya kara da cewa 'yan kungiyar Al-Qaeda ne ke kai hare-hare a wasu sassan kasar.

Shi ma shugaban rundunar sojin kasar, Alex Badeh, ya ce suna da shaidun da ke nuna cewa wasu baki daga kasashen waje na cikin wadanda ke kai hare-hare a kasar.

Shugaba Jonathan ya ce duk da haka jami'an tsaro na yin kokari wajen murkushe ta'addanci.

Karin bayani