Zamiya a cikin hamadar Niger

Image caption AbdelKader Baba ya ce rashin tsaro ya hana masu yawon bude ido zuwa Agadez

Wani mutum a jamhuriyar Niger ya bude kantin da ake sayar da kayan wasan zamiya a hamada.

Mutumin dai -- wanda a shekaru 30 da suka gabata ya lura cewa a kasuwannin kasar babu wanda ke sayar da irin wadannan kayayyaki -- ya bude kantin ne duk da yake babu masu sayen kayayyakin.

Har yanzu dai yana son bayar da haya ga mutanen da ke son yin wasan zamiyar hamada.

Ya baza kayayyakin ne a wani bangare na kantin - cikinsu har da wanduna da safa na yin zamiyar hamada.

Kazalika akwai wasu karafa - manya da kanana - masu launin ja, wadanda ke da fadin da mutum zai iya hawa kansu domin su zame da shi a wurin da ke da gangara.

Akasarin kayayyakin ya saye su ne a shekarun 1980.

Akwai kuma wani takalmi da ake zamiya da shi wanda sanya shi ke da matukar wahala, musamman a lokacin da ake fama da yanayin zafi.

Kantin yana birnin Agadez, wanda ke cikin hamada.

Yanayin zafin birnin yakan kai maki 45 a ma'aunin celsius.

Mai kantin, Abdelkader Baba, ya ce babu wanda ya taya kayansa tun shekarar 2007.

Ya ce shi kansa bai yi amfani da su ba tun wancan lokacin.

Ya kara da cewa ba zai yi wasan zamiyar hamada ba sai lokacin da masu yawon bude ido suka zo, yana mai cewa sun kauracewa birnin saboda matsalar satar mutane da hare-hare da 'yan bindiga ke kai wa.

Abdelkader Baba ya ce hakan ba zai hana shi ci gaba da gudanar da kasuwancinsa ba.

Image caption Babu wanda ya sayi kayan tun a shekarar 2007

Karin bayani