'Yan aware sun harbo helikoptar Ukraine

Hakkin mallakar hoto sergey esipov
Image caption Sojoji 14 sun mutu sakamakon harbo helikopta

Mayakan da ke goyon bayan Rasha a gabashin Ukraine sun harbo wani jirgi mai saukar angulu na daukar kaya na soji, inda suka kashe sojoji goma sha hudu, da suka hada da wani Janar.

Jirgin mai saukar ungulu na dauke ne da dakaru a kan hanyarsu ta zuwa wani sansani a kusa da garin Slovyansk dake hannun 'yan tawaye a lokacin da 'yan bindigar suka bude wuta.

Ana tafka kazamin fada a yankin Slovyansk tsakanin dakarun gwamnati da 'yan aware magoya bayan Rasha.

A yanzu haka ana tattaunawa kan yadda za a sako masu sa'ido na Tarayyar Turai da 'yan bindiga suka sace.

Karin bayani