'Yan bindiga sun kashe mutane 17 a Borno

Harin Gamboru Ngala a jihar Borno
Image caption Shugaba Jonathan ya umarci dakarun Nigeria su kaddamar da yaki kan Boko Haram

Rahotanni daga jihar Borno na cewa mutane 17 ne suka mutu a wani harin da aka kai kan kauyen Koma da ke bakin iyakar Nigeria da Kamaru.

Mazauna kauyen sun ce wasu 'yan bindiga a kan babura da wata mota ne suka kai harin, a lokacin da ake bikin aure inda suka kona rabin garin a ranar Alhamis.

Kawo yanzu babu tabbacin al'amarin daga jami'an tsaro, yayin da hare-hare tare da kona kauyuka da garuruwa ke neman zama ruwan dare a jihar ta Borno.

Ana dai zargin 'yan kungiyar Boko Haram da kai hare-haren, duk da yake kungiyar ba ta fito fili ta dauki alhakin kai hare-haren ba.