Google zai kera mota mai tuka kanta

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Motar na da wata na'ura a samanta da ke nazarin inda take

Kamfanin matambayi baya bata na Google ya sanar da cewa zai fara kera motar da zata dinga tuka kanta.

Google ya ce zai kirkiri motar ne, domin kawar da hadarin da mutane ke janyowa.

Kawo yanzu dai kamfanin na gyara wasu motocin da aka riga aka kera, kuma sun tuka kansu na nisan kilomitoci fiye da miliyan, yayin da kamfanin ke aiki kan fasahar.

Google na shirin kera daruruwan sabbin motoci masu tuka kansu da basu da sitiyari kuma ba burki, sai dai kawai abin latsawa da zai dakatar da motar ko ya sa ta ci gaba da tafiya.

Masu goyon bayan kera mota mai tuka kanta na cewa hakan zai rage yawan haddura.

Amma wasu masu binciken sun ce hakan zai kara cunkoson motoci a hanyoyin da ke birane.

Hakkin mallakar hoto Reuters