Tarihin Margayi Sarkin Gwoza

Hakkin mallakar hoto Yusuf Shettima
Image caption Margayi Sarkin Gwoza, Alhaji Shehu Mustapha Idrissa Timta

An haifi mai martaba Alhaji Shehu Mustapha Idrisa Timta ne a shekarar 1942, kuma da ne ga tsohon Sarkin Gwoza Alhaji Idrisa Timta.

Margayi Sarkin, ya soma karatu ne makarantar Elemantary ta Gwoza a shekarar 1948 kafin ya koma Makarantar Firamare ta Bama daga shekarar 1952 zuwa 1960.

Daga nan sai ya tafi makarantar Sakandare ta Maiduguri daga shekarar daga 1960 zuwa 1964.

Margayi tsohon Sarkin, ya soma aiki koyarwa a Gwoza kafin ya tafi Jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria inda ya karanta fannin Shari'a a shekarar 1968, daga bisani a shekarar 1972 ya samu takardar shaidar babbar diploma watau HND.

Alhaji Shehu Mustapha Idrisa Timta ya yi aiki tare da ma'aikatar shari'ar Arewa maso gabashin Nigeria har zuwa watan Oktoban 1981 da aka nada shi Sarkin Gwoza mai daraja ta uku.

Margayi Sarkin, ya zama Sarki mai daraja ta biyu a shekarar 1987 kafin a watan Junairun 2014, ya zama Sarki mai daraja ta daya.

Margayin ya rasu ya bar mata hudu da 'ya'ya 28 da kuma 'yan uwa da dama.

Karin bayani