Mutane 13 sun rasu a hadarin mota a Sokoto

Image caption Dubban mutane na rasuwa a duk shekara a Nigeria sakamakon hadarin mota

Hukumar kiyaye hadurra kan hanyoyi a Nigeria ta ce a kalla mutane goma sha uku ne suka kone kurmus yayin da wasu sha hudu suka samu raunukka a cikin wani mummunar hadarin mota kusa da iyakar kasar da Jamhuriyar Nijar.

Kwamandan Hukumar mai kula da jihar Sokoto Dr. Umar Aliyu Gummi ya shaidawa BBC cewar lamarin ya faru ne lokacin da wasu motoci biyu suka yi taho-mu-gama a kauyen Tudun Moyilla da ke kusa da garin Illela na jahar ta Sokoto.

Hadarin ya auku ne a cikin daren ranar Alhamis.

Lamarin ya jefa mutane da dama cikin juyayi da zullumi.

Sai dai wani mazaunin garin Illela wanda ya shaida lamarin ya ce adadin wadanda suke konen ya zarta abinda hukumomi suka bayyana

Karin bayani