Za a sako Meriam Ibrahim daga kurkuku

Meriam Ibrahim da maigidanta
Image caption Meriam Ibrahim da maigidanta

Jami'i mafi girma a ma'aikatar harkokin wajen Sudan ya ce, nan da 'yan kwanaki masu zuwa za a sako Meriam Ibrahim, matar nan da aka yanke wa hukuncin kisa bisa zargin yin ridda.

A cewar Abdullahi Alzareg, kasar Sudan tana tabbatar da 'yancin mutum na bin addinin da yake so, kuma gwamnatinsa ta sha alwashin kare Meriam Ibrahim din.

Kasashen duniya dai sun yi ta yin Allah wadai da hukuncin kisan da aka yanke mata.

A yanzu haka tana daure a gidan kaso, inda ta haifi jaririya a wannan makon.

Meriam Ibrahim tana aure ne da wani Krista.

An kuma yanke mata hukuncin bulala dari bisa zargin yin zina, saboda ta na auren wanda ba Musulmi ba.