An yi janai'zar Sarkin Gombe

Hakkin mallakar hoto Facebook
Image caption Masarautar Gombe dai na daga cikin manyan masarautun da ake da su a arewacin Najeriya.

An yi jana'izar Mai martaba Sarkin masarautar Gombe da ke Najeriya Alhaji Shehu Usman Abubakar, wanda ya rasu a ranar Talata bayan ya kwashe kimanin shekaru 30 a kan gadon sarauta.

An dai binne gawar marigayin ne a cikin fadar Gombe kusa da kuburburan sarakunan da suka gaba ce shi, bayan dubban mutane daga sassa daban-daban na kasar sun yi mata sallah da yammacin ranar Jumu'a.

Wakilin BBC Is'haq Khalid wanda ya halarci taron jana'izar ya ce an binne gawar basaraken ne cikin tsauraran matakan tsaro, yayin da talakawansa ke ci gaba juyayin rashinsa tare da yaba kyakkyawan halayensa.

''Yayin da ake jimamin rashin Mai martaba Sarkin Gombe, ga alama alhinin ya kara fadada bayan kashe mai martaba Sarkin Gwoza da ke jihar Borno; wanda wasu 'yan bindiga suka yi wa kwanton-bauna da tawagarsa a kan hanyarsa ta zuwa jana'izar sarkin na Gombe,'' Inji Shi.

Karin bayani