Peter Mutharika ya zama Shugaban Malawi

Sabon Shugaban Malawi Peter Mutharika Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sabon Shugaban Malawi Peter Mutharika

An rantsar da Peter Mutharika a matsayin sabon shugaban kasar Malawi, bayan an sami tsaiko wajen bayyana sakamakon zaben, wanda ya janyo tashen-tashen hankula da kuma zargin yin magudi.

Mista Mutharika ne ya lashe zaben da aka gudanar a makon jiya da kashi talatin da shidda cikin dari na kuri'un.

Shugaba mai barin gado, Joyce Banda, ita ta zo ta uku.

Ta yi kira ga magoya bayanta da su mutunta sakamakon.

Babbar kotun Malawin ta yi watsi da bukatar da Mrs Bandar ta gabatar, ta neman a sake kidayar kuri'u, bisa zargin an tafka magudi.

Peter Mutharika dai tsohon ministan harkokin wajen Malawin ne, kuma dan uwan tsohon shugaban kasar da ya rasu kan karagar mulki a 2012, watau Bingu wa Mutharika.