Yau ce ranar yaki da shan taba ta duniya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Taken bikin na bana sh ne '' A kara wa taba sigari.haraji.''

Yau ce ranar da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta kebe domin bukin yaki da shan taba sigari a duniya.

Manufar bukin dai ita ce jawo ra'ayin al'ummar duniya ga irin yadda amfani da ganyen tabar ya watsu a duniya da kuma irin lahanin hakan ke da ga lafiya bil'adama.

Bincike ya nuna akwai daruruwan miliyoyin mutane da ke shan taba sigari a duniya kuma akalla kimanin miliyan 6 daga cikinsu kan mutu a kowace shekara sakamakon kamuwa da cututtukan da taba sigarin ke janyowa.

A wannan ranar dai akan bukaci kame wa daga kowane irin amfani da ganye tabar na tsawon sa'o'i 24.

Karin bayani