An yankewa Dan Pele hukuncin shekaru 33

Image caption Edinho Pele zai zaman kaso

An yankewa Dan fitaccen dan wasan kwallon kafa na kasar Brazil din nan wato Pele hukuncin shekaru 33 a gidan kaso, saboda samun shi da karkata akalar wasu kudade da aka samu daga masu safarar miyagun kwayoyi.

Edinho Pele dai kamar mahaifinsa shi ma fitaccen dan wasan kwallon kafa ne da ya yi murabus, wanda ya ke kwararren mai tsaron raga a tsohon kulob din mahaifinsa da ke birnin Santos a shekarun 1990.

Wakilin BBC yace shekarar Edinho 5 a duniya ya tafi Amurka tare da mahaifinsa, a can ya sanya hannu kan kwantiragin fara wasan kwallon kafa a birnin New york.

Kame na farko da aka yi wa Edinho shi ne a shekarar 2005 da aka yanke masa hukuncin zaman Kaso, saboda samunsa da safarar miyagun kwayoyi da kuma alakar da ke tsakaninsa da wani shugaban masu safarar muggan kwayoyi a birnin Santos.

Sai dai ya musanta zargin da ake masa na safarar kwayoyin, inda ya ce ya san dai ya na ta'ammali da su.

Karin bayani