Matsi kan Qatar game da kwallon kafa

Nasarar Qatar
Image caption Nasarar Qatar

Wani babban jami'in kungiyar kwallon kafa ta duniya, FIFA, ya ce yana da ra'ayin a sake lale game da shirin karbar bakuncin gasar kwallon kafar shekara ta dubu biyu da ashirin da biyu, idan har zargin cin hancin da ake game da nasarar da kasar Qatar ta yi na karbar bakuncin, ya tabbata gaskiya.

Mataimakin shugaban FIFAR, Jim Boyce, yana mayar da murtani ne ga zargin da jaridar Sunday Times ta London ta yi.

Jaridar ta ce, ta sami takardun da ke nuna cewa, wani tsohon jami'in kwamitin zartaswar FIFAr dan kasar Qatar, Mohammed bin Hammam, ya biya miliyoyin daloli ga jami'an kwallon kafa don su goyi bayan takarar Qatar wajen neman shirya gasar kwallon.

Bin Hammam dai ya ki ya ce komi game da sabon zargin da ake masa.