Bam ya kashe mutane a Mubi

Hakkin mallakar hoto AFP

Rahotanni daga Najeriya sun ce wani bam ya tashi a garin Mubi dake arewacin Jihar Adamawa ya kashe mutane da dama.

Jami'an tsaro da mazauna garin sun ce an jefa bam din ne a wajen wani gidan kallon kwallo a garin.

Babu cikakken bayanin yawan mutanen da suka mutu, amma ance an kwashi gawawwakin mutane da dama.

Haka kuma mutane da yawa sun samu raunuka.

Wani wanda kanenshi ya ji rauni a wajen ya gaya wa Sashen Hausa na BBC cewa mutane da yawa sun mutu, wasu kuma sun jikkita. Sojoji sun je sun zagaye wurin da abin ya auku, inji wani mazauni garin.

Ya kuma ce da misalin karfe shidda na yamma ne ran Lahadi bam din ya tashi.

Jihar Adamawa dai na karkashin dokar ta-baci wanda aka kafa a jihar da sauran jihohin Borno da Yobe tun bara a sabilin hare-haren da 'yan Boko Haram keta kaiwa a yankin.

Karin bayani