Nijar: Kotu ta hana 'yan adawa zanga-zanga

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Bayan hukunci 'yan adawar sun yi wata gana wa karkashin jagorancin Seyni oummarou.

Wata babbar kotu a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar ta hana kawancen jam'iyun adawar kasar na ARDR gudanar da zanga-zangar lumanar da suka tsara yi a yau din nan.

Wannan dai shi ne karo na biyu da hukumomi a birnin Yamai ke hana 'yan adawar yin wannan zanga-zangar a cikin makonni biyu.

Gwamnatin kasar dai ta ce 'yan adawar na son amfani da zanga-zangar ne wajen kawo tashin hankali a kasar.

'yan adawar dai sun ce za su yi biyayya ga umarnin kotun, sai za su ci gaba da neman iznin yin zanga-zangar.

Karin bayani