Fyade: An tarwatsa masu gangami a India

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan mata da dama sun fada hannun masu fyade a india

A kasar India, 'yan sanda sun fesa ruwan zafi kan daruruwan masu zanga-zangar da ke neman a daina cin zarafin mata.

Masu zanga-zangar -- wadanda akasarinsu mata ne -- na yin jerin gwano ne a jihar Uttar Pradesh da zummar zuwa ofishin babban minista da ke birnin Lucknow don kai korafinsu.

Suna yin zanga-zangar ne bayan wasu mutane sun yi wa wasu 'yan mata fyade, kana suka rataye su a wani kauye da ke jihar a makon jiya, lamarin da ya jawo Alla-wadai daga sassan duniya daban-daban.

'Yan uwan 'yan matan da aka kashe sun ce sai da aka kwashe sa'o'i da dama kafin 'yan sanda su kai dauki.

An kama mutane biyar, cikinsu har da 'yan sanda biyu, wadanda ake tuhuma kan batun.

Karin bayani