Sarkin Spain Juan Carlos ya yi murabus

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Juan Carlos ya ce zai bai wa matasa waje domin su taka rawa

Sarkin Spain Juan Carlos ya yi murabus bayan ya shafe shekaru araba'in akan karagar mulki.

Cikin wani jawabi ta talabijin sarkin mai murabus ya yi godiya ga al'ummar Spain saboda irin goyon bayan da suka ba shi.

Sarki Carlos ya ce ya yi murabus ne domin bai wa sabbin-jini su ba da tasu gudunamawar wajen ci gaban kasar.

Yanzu haka dai dansa, Yarima Felipe ne zai gaje shi.

Karin bayani