Emefiele ya fara shugabancin CBN

Sabon shugaban babban bankin Nigeria, Godwin Emefiele ya fara aiki a ranar Talata, bayan karewar wa'adin Sanusi Lamido Sanusi.

Wasu a kasar na ganin tsohon shugaban bankin Zenith, zai dora ne kan manufofin wanda ya gabace shi.

Daya daga cikin kalubalen da ke gaban Emefiele shi ne kare darajar naira, ga mutumin da ya dauki bunkasa tattalin arzikin kasa da muhimmanci.

Shugaban Najeriya ya dakatar da Sanusi Lamido ne a watan Fabrairun da ya gabata, bisa zargin almubazzaranzi.

Ko da yake wasu na ganin dakatar da shi baya rasa nasaba da kwarmata batan dabon da $20 biliyan daga lalitar kamfanin mai na kasar NNPC.

Karin bayani