Kwanaki 50 da sace 'yan matan Chibok

'Yan matan Chibok a Najeriya Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption 'Yan matan Chibok a Najeriya

A Najeriya yau ne ake cika kwanaki 50 cif da sace 'yan matan nan sama da 200 a wata makarantar sakandare dake Chibok a jihar Borno.

Ba Najeriya kadai ba, sace 'yan matan, ya ja hankalin Kasashen duniya da dama.

A Najeriyar dai tun bayan sace 'yan matan an yi ta samun Kungiyoyi da suka taso wadanda ke matsawa gwamnati lamba na ganin an ceto wadannan 'yan mata daga Kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram wadda ta yi ikirarin sace su.

Hukumomin tsaron Najeriya dai sun ce suna bakin kokarinsu wajen ganin an ceto wadannan 'yan mata cikin koshin lafiya da kuma ransu.

Amma har yanzu kusan za a ce babu wani abu takamaimai da za a ce sun yi na kubutar da 'yan matan.