Sakamakon karshe na zaben Masar

Abdulfatah al-Sisi tsohon Jagoran sojin Masar Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Abdulfatah al-Sisi tsohon Jagoran sojin Masar

Sakamakon karshe na zaben shugaban kasar Masar ya tabbatar da gagarumar nasarar tsohon jagoran sojan kasar, Abdul Fatah Al Sisi.

Hukumar zaben kasar ta Masar ta ce, Al Sisi ya lashe kashi casa'in da shida da digo tara na kuri'un da aka kada, yayin da abokin hamayyarsa ya samu kashi uku cikin dari.

Sai dai kuma kashi 47 da digo 5 ne suka fito jefa kuri'a a zaben.

Cikin jawabin farko a matsayinsa na shugaban kasar, Al Sisi yace, lokaci yayi da za'a soma yiwa jama'a aiki.

Koda dai kafin a kai ga bayyana sakamakon zaben dama ana zaton Al Sisi ne zai lashe shi.

Karin bayani