Gwamnatin Kano ta yi watsi da nadin Waziri

Wani masallacin juma'a a Kano
Image caption Gwamnati na dakon kwamitin zartarwa na masarautar Kano kan batun

Sabani ya kunno kai tsakanin masarautar Kano da fadar gwamnatin jihar kan nadin sabon wazirin Kano.

Hakan ya biyo bayan watsin da gwamnatin ta yi na nadin Limamin masallacin juma'a na Fagge, Sheik Nasir Muhammad Nasir a matsayin wazirin Kano.

Mataimakin gwamnan jihar Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya gaya wa BBC cewa, bangaren kula da tsaro na gwamnatin ya fitar da rahoton cewa mutane ba su amince da nadin wazirin ba.

Gwamnatin Kano ta ce za ta dauki mataki matukar masarautar Kano ba ta warware nadin da ta yi ba.

A ranar Juma'ar da ta wuce ne Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero ya nada Sheikh Nasir a matsayin Wazirin Kano.