OIC na goyon bayan yaki da ta'addanci

Najeriya Boko Haram Hakkin mallakar hoto
Image caption Najeriya Boko Haram

Kungiyar kasashen Musulmi wato OIC ta nuna goyon bayan ta ga gwamnatin Nijeriya a yakin da take yi da ta'addanci a kasar.

Kungiyar ta kuma bayyana 'yan kungiyar Boko Haram a matsayin gungun 'yan ta'adda wadanda ta ce bai kamata a rika danganta su ba da addinin Musulunci.

Babban sakataren kungiyar ta OIC Eyad Ameen Madani ne ya bayyana haka a Abuja lokacin da ya jagoranci wata tawaga zuwa fadar gwamnati Nijeriya inda suka gana da shugaban kasar Goodluck Jonathan.

Eyad Ameen Madani ya kuma ce kasashe 57 mambobin kungiyar za su ci gaba da taimakawa Najeriya a fafitikar da ta ke yi na kawo karshen hare-haren ta'addanci a kasar.

Ya kuma yi kakkausar suka ga kungiyar Boko Haram da tace ayyukanta sun sabawa koyarwa addinin Musulunci.