Za a bude rumfunan zabe a Syria

Zabe a kasar Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zabe a kasar Syria

A kasar Syria nan gaba kadan ne a yau, za a bude runfunan zaben Shugaban kasa a yayin da ake cigaba da gwabza yakin basasa a kasar.

A karon farko cikin shekaru 50, dangin Assad na fuskantar kalubale daga wasu 'yan takara 2 da gwamnati ta amince da su - koda yake dai Shugaba Assad din ne ake hasashen zai samu nasara cikin sauki.

Hassan Al Nouri, daya daga cikin 'yan takarar, ya shaidawa BBC cewar, lokaci ya wuce da wani mutum guda zai cigaba da yanke shawara kan makomar Syria.

Za a gudanar da zaben ne a yankunan da gwamnatin kasar ke rike da madafun iko, kana akwai tsauraran matakan tsaro da aka dauka don yin fito na fito da duk wata barazanar harin 'yan tawaye.

Masu adawar kasar Syria da ke samun goyon bayan kasashen yammacin duniya sun yi Allah wadai da zaben a matsayin wani shirme inda suka yi kiran da a kaurace masa.