An soma bincike kan satar bayanan Merkel

Angela Merkel, Shugabar gwamnatin Jamus Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Angela Merkel, Shugabar gwamnatin Jamus

Masu gabatar da kara a Jamus sun soma bincike dangane da zargin satar bayanan wayar shugabar gwamnatin Jamus din, Angela Merkel da aka yiwa hukumar tsaron kasa ta Amurka.

Bankado batun bayanan wayar shugabar gwamnatin Jamus din da aka yi zargi Amurka tana yi ya lahanta hulda tsakanin gwamantin Amurkan da kuma ta Jamus.

Mai shigar da kara, Harald Range ya fadawa wani kwamitin majalisar dokoki cewa,"akwai zargin cewa, wasu jami'an leken asirin Amurka sun saci bayanai da leken asirin wayar salular shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, dan haka yanzu an soma bincike a kan wannan batu."

Batun dai na daga cikin irin batutuwan da Edward Snowden ya kwarmata.