Sojoji sun musanta agaza wa Boko Haram

Jami'an sojin Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ministan ya ce ko a batun 'yan matan Chibok gwamnati a tsaye take

Rundunar Sojin Najeriya ta musanta rahotannin cewa wata Kotun Soji ta samu wasu manyan jami'anta da laifin agaza wa 'yan Boko Haram.

Ma'aikatar tsaron kasar ta ce babu kanshin gaskiya a zargin da aka yi, cewa manyan jami'an da suka hada da wasu janar-janar guda 10 sun taimaka wa 'yan ta'addan.

Rundunar ta bayyana rahotannin da cewa karairayi ne da aka shirya, domin bata sunan sojojin a lokacin da aka shiga wani hali na tsaka-mai-wuya a kasar.

To amma ministan cikin gida na kasar Abba Moro ya ce yana da kyau da sojojin suka gano sojojin da ke hana ruwa-gudu a yakin da ake yi da masu tayar da kayar-bayan.