Jonathan zai nada Shekarau minista

Image caption A wannan shekarar ne Ibrahim Shekarau ya koma jam'iyyar PDP daga APC

Shugaban Nigeria Dr Goodluck Jonathan ya mika wa Majalisar dattawa sunan tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau domin a nada shi a matsayin minista.

Haka kuma, shugaba Jonathan ya mika sunayen Dr. Abdul Bulama daga jihar Yobe da Prince Dayo Adeyeye daga jihar Ekiti da kuma Steven Oruh daga jihar Delta don neman amincewar majalisar don ya ba su mukamin ministocin kasar.

A wannan shekarar ne dai tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya sauya sheka daga jam'iyyar adawa ta APC zuwa jam'iyyar PDP mai mulkin kasar.

A mako mai zuwa ne dai ake saran Majalisar dattawan za ta fara tantance sunayen mutanen da aka mika mata domin zama ministocin kasar.

Karin bayani