Musulmai na mawuyacin hali a CAR

Hakkin mallakar hoto HRW
Image caption Dubban 'yan gudun hijira daga Jamhuriyar Tsakiyar Afrika na shigowa Kamaru

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta bukaci hukumomi Jamhuriyar Tsakiyar Afrika da su ba Musulmai da ke zaune a kasar damar neman mafaka daga kasashe makwabta.

Rahotanni sun ce al'ummar musulmai da dama a kasar na cikin wani mawuyacin hali inda suka kosa su fice daga kasar.

Wannan na zuwa ne yayin da hukumomin agaji na Majalisar Dinkin Duniya suka bukaci karin tallafi domin shawo kan matsalar ayyukan jin kai da ake fuskanta.

A bangare guda kuma hukumomi a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiyar sun sanar da dakatar da musayar sakonni a rubuce ta wayar salula na wani dan lokaci domin daidaita al'amuran tsaro a kasar da ta dauki lokaci tana fama da rikicin addini.