Enugu ta tilasta wa 'yan arewa yin kati

Image caption Masu kare hakkin dan adam sun sha alwashin zuwa kotu

A Nigeria, gwamnatin jihar Enugu ta kirkiro wa al'ummar arewacin kasar mazauna jihar wani katin shaida, wanda aka tilasta wa kowannensu sanyensa a kan kudi N1000.

An kuma yi zargin cewa idan aka kama mutum ba shi da wannan kati, za a yi masa tarar kudi N5000, a kuma zarge shi da kasancewa dan kungiyar Boko Haram.

Sai dai wasu shugabannin 'yan arewan da kuma kungiyar kare hakkin bil'Adaman ta Civil Liberties Organization sun soki batun yin katin, har ma sun bayyana aniyar kai kara kotu a kan haka.

Sau da dama dai ana kama 'yan arewacin Nigeria da ke zaune a kudancin kasar, inda ake zarginsu da kasance wa 'yan Boko Haram, zargin da suka sha musanta wa.

Karin bayani