'Karar bam' a gidan Gwamnan Gombe

Gombe a taswirar Najeriya
Image caption Gombe a taswirar Najeriya

Rahotanni daga Gombe a arewacin Najeriya na cewa da yammacin yau wasu abubuwa sun fashe a kofar gidan gwamnan jihar, a wata mota dake gadin gidan.

Kawo yanzu dai babu cikakken bayani kan hasarar rayuka ko jikkata.

Mazauna birnin na Gombe dai sun bayyana cewa karar fashewar abin da ake kyautata zaton bam ne an ji ta ko ina a cikin birnin.

An ce a lokacin aukuwar lamarin, Gwamnan jahar Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo, ya na gidan amma dai yana nan lafiya kalau.

Kakakin gwamnan Malam Junaidu Usman ya musanta bayanin dake cewa bam ne ya fashe a kofar gidan gwamnan cikin motar masu tsaron gidan.

Wasu da suka shaida lamarin sun ce sun ga an kwashe wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa asibiti.