Amurka da Turai da Somalia sun gana kan siyasa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kungiyar al Shabab na ci gaba da fafatawa da sojojin gwamnatin Somalia da na Tarayyar Afrika

Jami'an Amurka da na Tarayyar Turai sun yi wani taron gaggawa tare da shugaban Somalia, Hassan Sheikh Mohamoud, domin tattauna tabarbarewar al'ammuran siyasa.

Haka kuma taron da aka yi a cikin wani jirgin ruwan yaki a kusa da gabar ruwan Somalian saboda dalilan tsaro, ya kuma duba halin da jama'a ke ciki a Somalia.

Babbar jami'ar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ayyukan agaji Valerie Amos, ta yi kira da a tattara dala miliyan 60 domin taimakawa kasar ta Somalia saboda kada ta sake fadawa cikin wani bala'i.

Ta ce kasashe masu bayar da agaji sun ba da kashi 19 kacal daga cikin 100 na alkawuran da suka yi.