An yi jana'izar Sarkin Kano Ado Bayero

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Margayin Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero

An yi jana'izar Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero wanda ya rasu a ranar Juma'a sakamakon doguwar jinya.

Dubun dubatar mutane ne suka halarci Jana'izar, inda aka yi masa Sallah a kofar fadar Kano.

Dan shekaru 83, Margayi Alhaji Ado Bayero na da kwarjini sannan kuma ana girmama shi a duk fadin Nigeria da wasu makwabtan kasashe.

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya bayyana kaduwa game da rasuwar, inda ya bayyana shi a matsayin mai son zaman lafiya wanda ya kulla dankon zumuncin da al'ummomi daban-daban a kasar.

Alhaji Ado Bayero ya hau sarautar Kano yana da shekaru 33, sannan ya yi mulki na tsawon shekaru 51.

Margayin tsohon Sarkin tsohon ma'aikacin banki ne kuma ya yi aikin dan sanda.

Ya kuma taba zama dan majalisar dokoki sannan kuma tsohon jami'in diplomasiya.

A ranar Juma'a 11 ga watan Oktobar 1963 ne kuma aka nada Alhaji Ado Bayero a matsayin sarkin Kano bayan rasuwar Sarki Muhammad Inuwa dan Sarkin Abas.

Alhaji Ado Bayero shi ne sarkin mafi dadewa a sarakunan Fulani a kano da suka fara mulki bayan jihadi a shekara ta 1807.

Hakkin mallakar hoto Getty

Karin bayani