Gwamnatin Kano ta sanar da rasuwar Sarki

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sarkin Kano ya rasu bayan doguwar Jinya

Mataimakin gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da rasuwar sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero a hukumance.

"Mun bayar da sanarwa ta rasuwar mai martaba Sakin Kano, Alhaji Dr. Ado Bayero yau (Ranar Juma'a) da asuba da misalin karfe hudu, kuma Allah ya jikansa. Muna addu'a Allah ya gafarta masa."

Dr. Ganduje ya kara da cewa, "Wannan rasuwa ce ba ta al'ummar jihar Kano kawai ba, Najeriya da ma duniya ga baki daya, saboda haka abin da ya wajaba a kanmu shi ne mu ci gaba da yi masa addu'a, Allah ya gafarta masa kuma Allah ya kyauta bayansa."

Mataimakin gwamnan ya sanar da rasuwar ce a gaban manema labarai a Kano.