Nigeria: An kama madugun 'yan awaren Biafra

Image caption 'yan awaren dai sun kwashe shekaru sama ga 50 suna fafutukar kafa kasar ta Biafra.

'Yansanda a birnin Enugu na kudu maso gabascin Najeriya sun damke shugaban wata kungiya mai fafutukar kafa jamhuriyyar Biafra bisa akidar addinin yahudancin,tare da wasu magoya bayansa 12.

Wannan dai ya biyo ne bayan da 'yan kungiyar ta Biafran Zaonist Federation suka yi yunkurin kutsawa cikin gidan rediyon jihar da nufin yin jawabi ga al'umma.

Akalla mutane biyu ne suka mutu yayin arangamar da aka yi tsakanin jami'an 'yan sanda da 'ya'yan kungiyar a harabar gidan Radiyon ranar Alhamis.

''Rundunar 'yansandan ta ce ta kuma kwace wasu abubuwa daga wurin 'ya'yan kungiyar da suka hada da litoci 25 na man fetur, da adduna da kwalabe da sauran miyagun makamai da kuma wasu faya-fayan CD 9 da ake jin suna kunshe ne da jawaban da suka so watsawa ta gidan radiyon'' Inji wakilin BBC a birnin Enugu.

Karin bayani