Yadda aka nada Alhaji Ado Bayero sarkin Kano

Hakkin mallakar hoto Getty

Sarkin Ban Kano Alhaji Mukhtar Adnan ya bayyana yadda suka zabi marigayi Alhaji Ado Bayero a matsayin sarki, ga karin bayaninsa kamar haka.

"Mun gode Allah da ya raya ni, zan ba ka amsar wannan tambaya, ba don haka ba, da ba za ka samu mai ba ka amsar tambayar ba.

Sarkin Kano Muhammadu Inuwa Allah ya masa rasuwa. Sai gwamnatin jihar Kaduna ta ce mu zabi sabon sarki, mu hudu: da madakin Kano Alh. Shehu Ahmed, da makaman Kano, Alh Bello Barwa, da sarkin dawaki mai tuta, Alh Bello Dandago, sai kuma ni sarkin ban Kano, Alh Muntari.

Aka tara mu, aka kai mu gidan Razdan, wato gidan gwamnati na yanzu kenan, aka ce ga ka'idodi da za ku duba, an yi hakan ne kuma bayan kwana guda da rasuwar sarkin kanon.

An ba mu ka'idoji da dama, na farko dai shi ne tilas sai mutum ya gaji sarautar, wato sullubawa kenan irin Ibrahim Dabo, na biyu tilas ya zama namiji, na uku ya zama balagagge cikakke wanda yake karbabbe ga jama'a, sannan mai halin kirki.

Akwai yayyensa da kawunnansa, duk mun bi su mun gani, mun yi la'akari da zamani da kuma meye ra'ayin jama'a, da kuma irin ayyukan da ya yi. Muka ga shi ya fi dacewa mu ba da sunansa.

Mu a bangarenmu ba wani wanda ya gaji sarauta, da ya zo ya same mu, ya ce mana don Allah yana son sarautar. Kyale mu kawai aka yi, muka yi zabenmu don Allah, da kuma yadda jama'a za su gamsu.

Hakkin mallakar hoto Manuel Toledo

Da magariba wajen karfe bakwai da rabi, gwamnan wancan lokaci ya kira mu ya shaida mana abin da za mu yi, kuma kafin karfe tara na wannan dare mun gama, daga nan muka sanar da gwamnan, ga wanda muka zaba, ya kuma gani, ya ce shi kenan. Ya amince zai gaya wa Kaduna, kuma duk abin da ta ce zai sanar da mu.

Washe gari gwamnan ya shaida wa Madaki cewa ya tara mu. Da hakimai da sauran jama'a da makada, a taru a fadar sarki. Yana da sakon da zai gaya mana daga Kaduna.

Muka hadu daga nan ya ce to zaben da muka yi na sarki, Firimiya ya amince cewa Alh Ado Bayero shi ne Sarkin Kano daga ranar, nan da nan sai aka yi ta tambari.

Kuma duk wannan abu fa da muka yi, shi sabon sarkin ba shi da labari. Kuma tun da muka zabe shi babu wata nadama da muka yi, sai ma alfahari, kuma har ya zuwa yau Kano ma ta san ba mu yi zaben tumun dare ba. "