Ana ci gaba da zanga-zanga a Brazil

Masu zanga-zanga a Brazil Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga-zanga a Brazil na bukatar gwamnati ta samar ababen more rayuwa.

'Yan sanda a kasar Brazil sun yi amfani da hayaki maisa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zanga ya yin da aka shiga rana ta biyu ta yajin aikin da tashashon jiragen kasa ke yi, lamarin da ya janyo cunkoson ababen hawa a birnin Sao Paulo.

Kusan rabi daga cikin tasashon jiragen kasa an rufe su, haka kuma akwai cakudewar jama'a da ababen hawa a titunan babban birnin kasar Brazilia inda za a faro gasar wasan kwallon kafa ta duniya a mako mai zuwa.

Ma'aikatan da ke yajin aikin dai na bukatar ayi musu karin albashi da a kalla kashi 10 cikin 100.

Sasantawa tsakanin gwamnati da kungiyoyin kwadago ta ci tura, haka kuma masu jagorantar zanga-zangar sun ce za a ci gaba da wannan gwagwarmaya har sai baba ta gani.